- Fusatattun matasa sun lakadawa fasto duka har sai da ya suma a garin Ibaji da ke jihar Kogi
- Hakan ya faru ne saboda faston ya hana matasan shiga coci su yi wani bautan dodon garin
- Bayan hana su shiga cocin matasan sun dawo da dare dauke da makamai suka masa duka
Wasu fusatattun matasa kimanin su 20 sun lakadawa wani fasto Michael Samson na cocin United Evangelical da ke jihar Kogi duka har sai da ya suma, rahoton Daily Trust.
An ruwaito cewa faston cocin da ke garin Iyano a karamar hukumar Ibaji ta jihar Kogi ya hana matasan gudanar da wani bauta da za su yi ne yayin biki da wani dodo a garin.
DUBA WANNAN: Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi
Rikicin ya barke ne a yayin da faston ya ce matasan ba za su shiga cocin ba.
Hakan ya fusata su, matasan suka koma gida suka dawo da muggan makamai suka far wa mutumin a yayin da ya ke barci.
A lokacin da ake hada wannan rahoton faston ya fara samun sauki a babban asibitin garin Idah.
KU KARANTA: An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja
Wata kwakwarar majiya ta ce wadanda suka yi wa faston duka na son yin wani bauta ne da alolin kasarsu da ake kira "Ane" a kasar Igala.
Faston ya hana su yin 'bautar' da za su yi inda ya ce ba nan da ya dace su yi ba.
"Bayan tafiyarsu, sun dawo da dare dauke da muggan makamai suka yi wa faston duka har sai da ya suma.
"Sun kai 20. Muna addu'ar kada wani abu ya samu dan uwanmu saboda yana cikin mawuyacin hali," in ji majiyar.
"An kai wa yan sandan Onyedega kara a karamar hukumar Ibaji," a cewar daya daga cikin yan uwan faston.
A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.
NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9k2lsbHFlYrO2v8CtmK2spaN6rq3TmqqaZZFiuLCzyGaqrqZdoa6srcOarppllpbAtbuMnaykmV2drrN50pqgZpyRYsaiedKupJpmmKm6rQ%3D%3D